<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>156</hymn_number>
<title>Zo Gare Ni, Masu Kaya LW156</title>
<lyrics>[V1]
 1) Zo gare ni, masu kaya,
 Masu shan wahala ma,
 In ji Yesu Mai Cetonmu,
 Ni in ba ku hutawa.

[V2]
 KORUS
 Akwai hutu kuwa mai daɗi,
 Wurin Ubangijinmu.
 Sai ku tashi, zo wurinsa,
 Zai saukad da kayanku.

[V3]
 2) Kayana fa marar nauyi,
 Karkiyata mai sauki ce.
 Sai ku koya a wurina,
 Za ku sami hutawa.
 Korus

[V4]
 3) Ga shi, kayanku da nauyi,
 Kuna shan wahala kuwa,
 In kun dogara ga Yesu,
 Shi zai ɗauke kayanku.
 Korus</lyrics>
</song>